✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta zanga-zangar #EndSARS a Abuja

Taruka da zanga-zanga ko tattaki sun haramta a birnin inda ake zargin masu zanga-zangar da take dokar COVID-19

Ministan Abuja, Muhammad Musa Bello ya haramta gudanar da zanga-zangar #EndSARS a fadin birnin na tarayya.

Kwamitin Tsaro na Abuja ya haramta dukkannin nau’ikan taruka, zanga-zanga ko tattaki a kan titunan da ke fadin Birnin Tarayya, sannan ya zargi masu zanga-zangar da take dokar kariyar COVID-19.

“Saba dokokin na barazana ga rayukan masu zanga-zangar da saukar mutanen da ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

“Dokar kariyar COVID-19 kan taron jama’a ta wajabta ba da tazara, auna zafin jiki, sanya takunkumi da sauransu wadanda dukkaninsu masu zanga-zangar ba sa yi”, inji ministan.

Sanarwar da kakakinsa Anthony kakakinsa Ogunleye ya fitar ta jaddada aniyar Hukumar Birnin Tarayya na kare rayuka a dukiyoyin jama’a.

Taron majalisar tsaron, a cewarsa, ya samu halarcin shugabannin hukumomin tsaro, shugabannin addinai, sarakuna, shugabannin kananan hukumomi da manyan jami’an gwamanti.

Zanga-zanga #EndSARS da ke ci gaba duk da cewa gwamanti ta amince ta biya dukkanin bukatun masu zanga-zangar ya haddasa cunkoson ababen hawa musamman a shataletalen Berger, inda masu zanga-zangar suka yi sansani.

A ranar Laraba, ‘yan daba dauke da makamai sun kai wa taron masu zanga-zangar hari inda suka raunata mutane da dama suka kuma lalata motoci.

Masu zanga-zangar na neman gwamanti ta soke rundunar ‘yan sanda na SARS mai yaki da ayyukan fashi da kuma wa aikin dan sanda kwaskwarima.