✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta yin dariya na tsawon kwana 11 a Koriya ta Arewa

An kuma haramta wa ’yan kasar yin cefane dungurungum a ranar 17 ga watan Disamba

Koriya ta Arewa ta haramta wa ’yan kasarta yin dariya, shan giya ko yin duk wani abu da ke nuna farin ciki na tsawon kwana 11.

An dauki matakin ne domin bikin cika shekara 11 da rasuwar tsohon Shugaban Kasar, Kim Jong II.

Hukumomin kasar ne suka bayar da dokar domin alhinin mutuwar tsohon Shugaban, wanda ya mulki kasar tsakanin shekarar 1994 zuwa 2011.

Bayan rasuwarsa ne dai shugaba mai ci, Kim Jong Un, wanda shi ne na uku a cikin kananan ’ya’yansa, ya karbi ragamar mulkin kasar.

Wani dan kasar mazaunin birnin Sinuiju, ya shaida wa gidan rediyon Free Asia cewa, “A iya tsawon lokacin alhinin, ba mu da ikon shan giya, yin dariya ko aikata duk wani abin jimy dadi.

“A baya, duk wadanda aka taba kamawa sun karya dokar, an yanke musu hukunci a matsayin masu aikata babban laifi, inda aka batar da su, babu wanda ya kara jin ko da labarinsu.

“Ko da wani a danginku ya mutu, ba ka da ikon yin kuka da karfi, kuma ba za a fitar da gawarsa ba sai wa’adin kwanakin ya cika.

“Ko bikin murnar zagayowar ranar haihuwa ba za a yi ba tsawon lokacin,” inji shi.

Majiyar ta kara da cewa, an kuma haramta wa ’yan kasar yin cefane dungurungum a ranar 17 ga watan Disamba, wacce ita ce ainihin ranar da tsohon Shugaban ya rasu.