Montana ta zama jihar ta farko a Amurka da ta haramta amfani da manhajar sadarwar zamani ta TikTok da China ta kirkira.
Wannan ya biyo bayan sa hannu da Gwamna Greg Gianforte na jam’iyyar Republican, ya yi kan kudirin dokar a ranar Laraba.
- Muna binciken gwamnan Zamfara kan N70bn —EFCC
- DSS ta tabbatar da tsare Baffa Hotoro kan batanci ga Annabi
“Don kare bayanan sirri na al’ummar Montana daga Jam’iyyar Kwaminisanci ta kasar Sin, na dakatar da Tiktok a Montana,” kamar yadda Gianforte ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan sanya hannu kan kudirin.
Sabuwar dokar ta hana jama’ar jihar amfani da manhajar nan take kuma duk wanda aka samu da laifin karyar dokar zai biya tarar Dala 10,000.
Wadanda ba za su fuskanci hukunci ko tara ba su ne wadanda suke da TikTok a wayoyinsu tun tuni, amma sabbin masu amfani da shi za su fuskanci tara da hukunci.
Masu manhajar TikTok har yanzu ba su ce komai ba kan sabuwar dokar da jihar ta sanya.
Ana sa ran za a shigar da kara na kalubalantar haramcin da aka yi kan ’yancin fadin albarkacin baki.
TikTok wanda mallakin kamfanin Byte Dance na kasar China ne, an riga an dakatar da amfani da shi a kasashen Kanada da Australia da New Zealand da Biritaniya da Amurka, saboda zargin nadar bayanan matsalolin tsaro ta yanar gizo.
Manhajar na da sama da mutum biliyan daya a duniya da ke amfani da shi.
Yana haifar da fargabar cewa hukumomin China da ma’aikatan sirri na iya amfani da manhajar don tattara bayanan sirri na kasashe.
Tun a baya kamfanin ya yi watsi da irin wadannan zarge-zarge da ake yi masa.