✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta amfani da lasifika a Masallacin Harami

Sautin sallar jam'i ya takaita zuwa cikin masallaci, an kuma kayyade karar lasifika

Kasar Saudiyya ta haramta yin amfani da lasifikokin da ke waje a Masallacin Harami da sauran masallatai a yayin sallar jam’i.

Ministan Harkokin Musulunci da Da’awa na Saudiyya, Dokta Abudllateef Al Sheikh ya ce an “takaita amfani da lasifikokin da ke wajen [Masallacin Harami da sauran] rassan ma’aikatar zuwa kiran sallah da tayar da Ikama kadai, sannan karar lasifikokin kar ta wuce maki uku na sauti.”

Ma’aikatar ta ce umarnin ya dace da fatawar Sheikh Muhammad bin Saleh Al-Uthaymeen da kuma Sheikh Saleh bin Fawzan Al-Fawzan wanda babban mamba ne a Kwamitin Fatawa, da sauran manyan malamai da suka bayar sama da shekara 20 da suka gabata.

Sanarwar ta ce, “Tun da isar da sautin liman a yayin sallar jam’i ya taikata ne zuwa ga mutanen da ke cikin masallaci, babu dalilin isar da sautin ga mutanen da ke gida.

“Sannan kuma rashin girmamawa ne ga Alkur’ani a sanya karatunsa a lasifika alhali ba a sauraron karatun Alkur’anin da ke fita a lasifikar.”