Ministan Birnin Tarayya, Muhammad Musa Bello ya sanar da haramta gudanar da Sallar Idi a Babban Filin Idi na Kasa da ke birnin.
Sanarwar tasa na zuwa ne a yayin da al’ummar Musulmi ke shirye-shiryen Sallah Karama, da ake sa ran yi a ranar Laraba ko Alhamis.
- An dawo da dokar kullen COVID-19 a Najeriya
- Karamar Sallah: ‘Ba za a ga wata ranar Talata ba’
- An yi fashi a kusa da Fadar Shugaban Kasa
- Zakatul Fidr: Yadda ake fitar da Zakkar Kono
“Ana umartar mutane su yi Sallar Idi a harabar masallatan Juma’ar unguwanninsu, a kuma rage yawan masu shiga masallaci zuwa kasa da kashi 50%.
Sanarwar ta kuma umarci a rufe daukacin wuraren shakatawa da na bude ido a lokacin shagulgulan sallar wadda ta ce a takaita gudanar da su zuwa cikin gidaje.
“Wajibi ne kuma mahukunta na addini su kula da shige da ficen masu ibada, su kuma tabbatar da kiyaye matakan kariya na sanya takunkumi, ba da tazara, da kuma wanke hannu.
“Bukukuwan Sallah kuma a takaita su zuwa cikin gidaje, yayin da wuraren shakatawa za su kasance a rufe,” inji sakon.
Sanar ta jajibirin sallah, na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan Gwamnatin Tarayya ta sanar da dawo da dokar hana taruwar mutane fiye da 50 da rufe wuraren taruwar jama’a domin takaita yiwuwar sake karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19.
Kakakin Ministan na Abuja, Anthony Ogunleye, ya ce Hukumar Gudanarwar Birnin Tarayya (FCTA), ta dauki matakin ne bayan zaman da Ministan ya jagoranta da Majalisar Limaman Abuja, karkashin jagorancin Imam Tajudeen Adigun.
Ya ce zaman nasu ya tattauna ne kan hanyoyin da za a bi wajen gudanar da bukukuwan Karamar Sallar.