An hana ’Yar Arewa guda daya tilo da Majalisar Datattawa ta tantance a matsayin kwamishinan zabe, Dokta Asma’u Sani Maikudi takardarta ta daukar aiki saboda matsin lambar wasu da ke son mukamin nata a fadar shugaban kasa.
Sunan Dokta Asama’u daga jihar Katsina wacce Shugaba Muhammadu Buhari ya zaba a cikin watan Maris din da ya gabata tare da wasu mutum 26 su cike guraben da aka warewa jihohinsu, ya tsallake dukkanin matakan da suka kamata har da matakin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya da Hukumar Da’ar Ma’aikata bayan Majalisar Dattawa ta tantance ta a ranar 20 ga watan Juli.
Bincike ya nuna cewa duk da cewa Shugaba Buhari ya zabe ta saboda cancanta amma wadansu masu karfin fada-a-ji a fadar shugaban kasa ba su ji dadin zabenta ta wakilci jihar Katsina ba.
Majalisar Dattawan ta raba tanatance wadanda aka mika sunayensu kashi biyu inda suka tantance sunayen kashi na farko a ranar 1 ga watan Juni.
Da Aminiy ta tuntube ta, Dokta Asma’u Maikudi, ta ce tana sane cewa abokanen aikinta sun karbi takardarsu ta aiki.
“An ummarce mu mu karbi takardarmu ta daukar aiki daga ofishin mai taimakawa shugaban kasa kan al’amuran majalisa a ofihin sakataren gwamnati kafin rantsar da mu amma da muka je can takardu bakwai kawai aka iya bayarwa aka ce tawa ta bata kuma aka gaya mani cewa ummarni aka bayar daga sama”. Inji ta.
Da aka tuntube shi kan lamarin Daraktan Yada Labari a Ofishin Sakataren Gwamnati, Mista Bolaji Adebiyi ya ce ba a sanar da shi lamarin ba.
Amma da aka ce masa sauran kwamishinonin da ka tantance tare da Dokta Asma’u tuni suka karbi takardunsu na daukar aiki, sai ya ce ba shi da labari amma zai bincika yau.