Gwamnatin Jihar Kano ta ce daga yanzu babu wani gida ko fili da za a sake sayarwa ko bayar da hayarsa a Jihar ba tare da samun sahalewa ko masaniyar Hakimi ko wakilansa ba.
Umarnin, a cewar wata sanarwa da kakakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji ya fitar ranar Asabar, yunkuri ne daga cikin irin hobbasan da gwamnati ke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
- ‘Bai kamata Turanci da Lissafi su zama dole wajen samun gurbin karatu ba’
- An kama ma’aurata sun shirya wa jaririn da suka sace biki
Sanarwar ta ce an yanke shawarar yin hakan ne saboda a taimaka wa aikin da sojoji ke yi na fatattakar ’yan bindiga daga kasar nan.
Sakataren Gwamnatin ya kuma ce, “Wannan umarnin ya biyo bayan ci gaba da kai hare-haren da ake yi a kan bata-gari, wanda ya zo daidai da shirin Gwamnatin Tarayya na kawo karshen ayyukan ta’addanci da na ’yan bindiga a wasu sassa na Najeriya.
“Matakin zai tilasta wa wadannan ’yan ta’addan su fara neman mafaka a Jihohi makwabtan wadanda ake wannan aikin a cikinsu, ciki kuwa har da Kano,” inji sanarwar.
Daga nan sai gwamnatin Jihar ta yi kira ga dillalai da babbar murya kan su bi umarnin sau da kafa, tana mai cewa za ta dauki yin kunnen uwar shegu da shi a matsayin hada baki da bata-garin wajen yi wa yunkurinta na samar da tsaro zagon kasa.