Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya dakatar da dukkan sarakunan gargajiyar jihar daga bayar da kowacce irin sarauta har sai sun sami amincewar gwamnati.
Umarnin dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Zailani Bappah ya fitar a ranar Laraba.
- LABARAN AMINIYA: An Kashe Jagoran CAN Da Wasu Mutum 5 A Kaduna
- A karo na 5 a 2022, wutar lantarkin Najeriya ta sake daukewa gaba daya
Umarnin na zuwa ne ’yan kwanaki bayan gwamnatin jihar ta dakatar da basaraken ’Yandoton Daji, Alhaji Aliyu Garba-Marafa, saboda nada kasurgumin dan bindiga, Ado Aleiro sarautar Sarkin Fulanin masarautar.
Lamarin dai ya yi ta jawo suka da Allah-wadai daga sassa daban-daban na Najeriya, inda wasu ke ganin yanayin a matsayin wani yunkurin karfafa musu gwiwa.
Amma a cewar sanarwar, “Dukkan sarakuna da manya da kananan Hakimai ana umartar su da cewa daga yanzu ole ne su nemi amincewar gwamnatin jiha kafin su bayar da kowacce irin sarauta.
“Hakan ya zama wajibi saboda mu magance bayar da sarautar ba kai ba gindi.
“Dole ne a yi wa wannan umarnin biyayya, bijire masa kuma zai haifar da daukar mummunan mataki a kan mutum,” inji sanarwar.