✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hana malamai wa’azi saboda sukar juna a Pakistan

Gwamnatin lardin ta dakatar da malaman yin wa'azi na tsawon watanni biyu.

Hukumomi a lardin Sindh na ƙasar Pakistan, sun hana malaman Addinin Musulunci fiye da 140 yin wa’azi har na tsawo wata biyu.

Hukumomin sun ce sun ɗauki matakin ne, don kauce wa ɓarkewar rikici, sakamakon sukar juna da malaman ke yi wa junansu.

Pakistan ƙasa ce da mabiya ɗariƙar sunna suka fi yawa, kuma ƙasar na fuskantar rikici tsakanin ɓangarorin addini a cikin watan Muharram.

Da yawan malaman su kan sukar mabiya mazhabar Shi’a marasa rinjaye a ƙasar, inda su ma ke mayar da martani, lamarin da ya fara haifar da ruɗani.

Wani jami’in gwamnatin ƙasar, ya ce dokar ta haramta wa malaman tafiye-tafiye da yin wa’azi har na tsawon wata biyu don hana sukar mazhabobinsu.

Haka kuma gwamnatin lardin ta kuma buƙaci gwamnatin ƙasar ta dakatar da wasu shafukan sada zumunta a kawanaki 10 na farkon watan.

Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnatoci a ƙasar ke ɗaukar irin wannan mataki ba.