✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hana magoya bayan Super Eagles yin kade-kade da bushe-bushe a Brazil

Rahotanni da ke fitowa daga gasar cin kofin duniya da yanzu haka ke gudana a Brazil sun nuna Hukumomin shirya wasan kwallon kafa a kasar…

Dokta Rafiu LadipoRahotanni da ke fitowa daga gasar cin kofin duniya da yanzu haka ke gudana a Brazil sun nuna Hukumomin shirya wasan kwallon kafa a kasar sun hana magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya da ma wasu kasashe yin amfani da kayayyakin kide-kide da bushe-bushe a yayin da wasa ke gudana.
Kamar yadda shugaban magoyua bayan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Dokta Rafiu Ladipo ya sanar, ya ce an kwace musu kayayyakin da suke yin kida da waka don goya wa Najeriya baya ne a ranar Litinin da ta wuce a lokacin da suke kokarin shiga filin wasa don ganin yadda za ta kaya tsakanin Najeriya da Iran.
Ya ce kimanin magoya bayan kungiyar 300 ne suka halarci Brazil don marawa Najeriya baya a gasar amma abin bakin ciki suna gab da shiga filin wasa sai jami’an hukumar FIFA suka karbe musu.  Ya ce jami’an sun fada musu cewa kayayyakin kide-kiden da bushe-bushen suna kawar da hankalin jama’a da kuma ’yan kwallon ne dalilin kenan da ya sa suka karbe su daga hannunsu.
Sai dai shugaban ya ce ba su taba samun umarni daga Hukumar FIFA a kan hana su amfani da kayayyakin kida a filin wasa ba kuma shekaru da dama kenan suke halartar gasar cin kofin duniya a kasashe daban-daban amma sai a wannan karo aka hana su amfani da su a Brazil.
Ya bayar da tabbacin za su rubutu koke na musamman ga Hukumar FIFA a kan hana su amfani da kayayyakin da suke jin za su karfafa wa kasarsu gwiwa a lokacin gasar.

Wasannin Yau Da Gobe:
Juma’a  20 Ga Yuni, 2014
Italy da Costa Rica          Biyar na Yamma  
Switzerland da France         Takwas na dare
Honduras da Ecuador         Sha daya na dare
Asabar 21 Ga Yuni, 2014
Argentina da Iran         Biyar na yamma
Germany da Ghana         Takwas na dare
Nigeria da Bosnia-Herzegobina Sha daya na dare