Wani rahoton ya gano cewa akalla mutum 348 ne suka rasa rayukansu sakamakon munanan hare-hare a sassan na Najeriya a watan Disamban 2020, yayin da wasu 411 kuma aka yi garkuwa da su.
Rahoton, wanda wata kungiya mai zaman kanta, Nigeria mourns, ta fitar ranar Litinin ya ce 315 daga cikin 348 din da aka kashe fararen hula ne, 33 kuma jami’an tsaro.
- Matar aure ta kashe budurwar da mijinta zai aura
- Duk wanda ya shiga jihar Kogi ya kubuta daga COVID-19 -Yahaya Bello
Kungiyar ta ce ta tattara alkaluman rahoton ne daga rahotannin da aka wallafa a jaridu da majiyoyin iyalan wadanda lamarin ya shafa.
Jihar Borno, wacce rikicin Boko Haram da ISWAP ya fi addaba na kan gaba a cikin jihohi 27 da rahoton ya bayyana, inda aka kashe akalla mutum 70.
Sauran jihohin sun hada da mutum 64 a Kaduna, 26 a Neja, 24 a Katsina, 23 a Ogun, 19 a Zamfara, 17 a Binuwai da Edo, 14 a Delta, 13 a Ebonyi.
An kuma kashe takwas a Adamawa, shida a Oyo da Ondo, sai biyar a kowanne daga jihoihn Bayelsa, Legas da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Sauran sun hada da mutum hudu a Ribas da Filato, uku a Imo, Kuros Riba da Kogin da Jigawa, biyu a Taraba da Anambra, sai kuma mutum daya a jihohin Osun da Kano da Enugu.
Rahoton ya kuma nuna cewa daga cikin adadin, mutane 136 ’yan bindiga ne suka hallaka su, 66 kuma wadanda ake zargin ’yan Boko Haram da ISWAP ne, sai kuma 60 da ake zargin ’yan kungiyoyin asiri ne suka yi sanadiyyar mutuwarsu.
Bugu da kari, rahoton ya ce rikice-rikicen kabilanci sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 41, wasu mutum 30 kuma an kashe su a daidaikunsu, takwas makiyaya sai kuma bakwai masu daukar doka a hannunsu suka hallaka.