✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hallaka ɗan bindiga a iyakar Abuja

Rundunar ta gano maɓoyar 'yan bindigar tare da kai musu samame.

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja sun hallaka wani ɗan bindiga tare da kama wasu uku a yankin Chikara da ke iyaka da Jihar Kogi da Abuja.

Kwamishinan ’yan sandan birnin tarayya, CP Benneth Igweh ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.

Ya ce rundunar ta kai samame maboyar ’yan bindigar da aka gano a dajin Chikara.

Waɗanda ake zargin uku da suka shiga hannu sun haɗa da Mahammadu Isa, mazaunin ƙauyen Dantata da ke Abuja, Likita Idris, ɗan asalin Jihar Kogi da Isiyaku Muhammadu, shi ma daga Jihar Kogi.

“Dakarunmu sun yi artabu da ’yan bindigar. Sai dai ’yan sandan sun yi musu ƙawanya, inda aka kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigar mai suna Abdusallam Abdulkadir,” in ji shi.

A cewarsa, mutanen uku da ake zargin ’yan bindiga ne, sun amsa cewar suna da hannu a wasu hare-hare da aka kai birnin tarayya da kewaye.

Ya ce sun ƙwato makamai da suka haɗa da bindigar gida, harsashi guda biyu, wuƙaƙe, da kuma layu.

Kwamishinan, ya ce rundunar na ci gaba da gudanar da bincike, inda ga nanata ƙudurinta na tabbatar da tsaron mazauna birnin tarayya.

Ya kuma yi kira ga mazauna Abuja da su yi taka-tsan-tsan tare da kai rahoton duk abin da ba su yarda da shi ba ta hanyar tuntuɓar lambobi kamar haka; 08032003913, 08028940883, 08061581938, da kuma 0705733765.