✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haifi yarinya da kafa uku da hannuwa hudu

An haifi wata yarinya da kafa uku da hannuwa hudu, inda ta yi kama da hallittar ’yan biyu, sai dai dayan babu kai. Lamarin ya…

An haifi wata yarinya da kafa uku da hannuwa hudu, inda ta yi kama da hallittar ’yan biyu, sai dai dayan babu kai.

Lamarin ya faru ne a Unguwar dansoda da ke garin Birnin Yero a hanyar Kaduna zuwa Zariya a jihar Kaduna.

Kakan yarinyar, Malam Kabiru Ahmadu ya shaida wa Aminiya cewa, “Malama Hauwa’u Jamilu wacce aka fi sani da Gambo ce ta haifi jaririyar a ranar Larabar makon jiya da karfe biyar na yamma kuma tana cikin koshin lafiya. Sai dai ba mu samu damar kai yarinyar asibiti ba domin a duba ta. Amma muna shirin yin hakan don ganin a yi mata tiyata don a cire barin rabin jaririn da ke manne da cikinta.”  

Ya kara da cewa, “Ni na haifi mijinta Jamilu Kabiru kuma wannan shi ne haihuwarta ta uku inda sauran biyu suke nan cikin koshin lafiya. Wannan ne kadai haihuwar da ta zo da ’ya mai ban al’ajabi. Abin da da ya sa ba mu je asibiti ba na har bayan kwana biyu da haihuwar shi ne don ba mu da karfi.” 

Malam Kabiru Ahmadu ya ce sun je wurin wani dan uwansa da ke aiki a asibitin Gwarzo a Jihar Kano inda aka tura su Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano. 

Wani likitan tiyatar yara da bai son a ambaci sunansa ya shaida wa Aminya cewa aiki ne da yake daukar lokaci kafin a yi shi, saboda sai yarinyar ta yi kwarin jiki da na kashi kafin a yi aikin. “Abu mai hadari a irin wannan aiki shi ne idan kayan ciki kamar hanji da tumbi da sauransu guda daya ne, to yana da hadari matuka,” inji shi.

Wata likitan mata ta shawarci mata a kowane kauye suke su tabbatar suna zuwa awon ciki da daukar hoton cikin don sanin irin abin da suke dauke da shi a ba su tallafi a kan lokaci.