✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

An haifi yara 2.7m a Katsina cikin shekara 5 – Hukumar Kidaya

Alkaluman dai sun zarce na Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS).

Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta ce an haifi yara kimanin 2,757,833 tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021 a Jihar Katsina.

Mai rikon mukamin Darakta a sashen hulda da jama’a na hukumar, Isiaka Yahaya, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa ranar Litinin.

Ya ce ta hanyar amfani da wata manhajar tattara alkaluman haihuwa a Najeriya mai suna RapidSMS, bayanai sun nuna a jihar ta Katsina an samu haihuwa 542,368 a shekarar 2017, sai 489,488 a 2018, 474,068 a 2019, 499,843 a 2020, yayin da aka samu 752,066 a shekarar 2021.

Ya ce alkaluman sun zarta wadanda Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta tattara.

“Alkaluman haihuwar da suka fito daga NBS sun rage ainihin adadin matuka, la’akari da karuwar haihuwar da ake samu a cibiyoyin yin rajistar guda 201 da ke fadin jihar, kuma suke yin rajistar kyauta.”

Ya ce karuwar yawan rajistar haihuwar, kamar yadda Kwamishinan Hukumar mai kula da Jihar ta Katsina, Injiniya Bala Banye ya tabbatar, ya samu ne da gudunmawar gwamnatin jihar da kungiyoyi masu ba da tallafi da kuma masu rike da sarautun gargajiya.