An gurfanar da wasu ’yan mata biyu gaban kotun bisa zargin yunkurin kashe Gwamnan Adegboyega Oyetola na Jihar Osun.
Dan sandan mai gabatar da kara John Idoko ya shaida wa Kotun Majistare mai zamanta a Osogbo cewa ’yan matan na daga cikin mutanen da suka fasa babban shagon kasuwanci a garin.
- An ba wadanda suka saci kayan tallafin Osun sa’o’i 72 su dawo da su
- An cafke dan sanda da satar waya da kudi a Osun
- Yadda kungiyar IPOB ta kashe Musulmai da sunan #EndSARS —Okonkwo
- Hatsarin mota ya salwantar da rayukan fiye da mutum 20 a Osun
Ya ce an hada baki da su aka yi yunkurin kashe gwamnan ta hanyar harbi da bindiga da kuma jifa da duwatsu.
Dan sandan ya ce ’yan matan sun fasa wani babban shagon na Ashiru Ibrahim Olayrmi, suka sace kwamfuta da wayoyin hannu da darajarsu ta kai N3,568,000.00.
Laifukan a cewarsa, sun saba da kundin laifuka na jihar na 2020 karkashin sashi na 516, 320 (1) da 451, 414 da kuma 390.
Wadanda ake zargin sun musanta aikata abin da ake tuhumar su da aikatawa sannan lauyansu ya bukaci kotun da ta ba da su beli.
Amma alkalin kotun, Mai Shari’a Olusegun Ayilara, ya hana tare da umartar a ci gaba da tsare su a kurkuku na Ilesa zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba 2020.