Wata Kotun Majistare da ke zamanta a yankin Ejigbo na Jihar Legas, ta bayar da belin wata mata mai shekara 29 kan kudi N300,000 bayan an gurfanar da ita kan laifin gallazawa wata makwabciyarta.
Alkalin Kotun, Mr E. O. Ogunkanmi, ya kuma umarci matar da ake tuhumar da ta kawo mutane biyu da za su tsaya mata a matsayin jingina.
- Ya saki matarsa saboda ta fiye zafin rai
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 25 a wani turnuku
- An sa dokar kayyade zancen samari da ’yan mata a Kano
Mutanen biyu da zai kawo su kasance ma’aikatan gwamnati tare da gabatarwa da kotu takardunsu na shaidar biyan gwamnatin Legas haraji.
Matar da ake tuhuma ana zarginta da laifukan da suka hada da cin zarafi da tayar da zaune tsaye wanda kuma duk ta musanta su a gaban kotun.
Tun da farko dai jami’in dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Benedict Aigbokhan, ya shaida wa kotun cewa, matar ta aikata laifin ne da misalin karfe 10.00 na ranar 16 ga watan Fabarairun 202.
Aigbokhan ya ce matar da aikata laifin ne a wani gida mai lamba 12 da ke kan titin Kwaleji a yankin Ipaja na Jihar Legas.
Ya ce laifin da matar ta aikata yana cin karo da wasu sassa na kundin dokokin manyan laifuka na Jihar Legas.
A karshe dai Alkalin Kotun ya dage zaman sauraron shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Afirilun 2021.