✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gurfanar da tsohon da ya yi barazanar kashe wata da adda a gaban kotu

Ana zargin da ne da barazanar kashe ta da adda

An gurfanar da wani tsoho mai shekaru 80 mai suna Ayoola Adeqole ranar Litinin a gaban kotun Majistare da ke Ile-Ife a jihar Osun, bisa tuhumarsa da barazanar kashe wata mata.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Adesina Elijah, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne ranar 22 ga watan Afrilun 2022, da misalin karfe 9:00 na dare, a kauyen Ayekoka da ke garin Ile-Ife a jihar Osun.

Elijah ya ce tsohon ya yi barazanar kashe wata mata ne mai suna Adekunle Bose da adda, bayan shiga wata gonar Koko da ke karkashin kulawarta ba da izini ba.

Haka kuma, ya ce Ayoolan ya yi wa wani mai suna Fayenuwo Pelumi dukan tsiya da falankin katako, hadi da sace kokon da goro da jan inibi da kudinsu ya kai Naira 230,000 mallakin Adekunle.

Laifin dai a cewarsa ya saba wa sassa na 81 da 86 da 351 da 383 da 388 da 390(9) na kundin manyan laifukan jihar Osun na 2002.

To sai dai Ayoola ya musanta zargin, inda kuma Alkalin kotun, Mai Shari’a A. I. Oyebadejo ya ba da belinsa kan kudi Naira 100,000 da masu tsaya masa da ke da makamancin kudin.