Rundunar ’yan sandan Jihar Ekiti, ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 25 kan zarginsa da uzzura wa al’ummar unguwa da shiga hakkinsu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito jami’in dan sanda, Insfeta Olubu Apata yana shaida wa kotun cewa, matashin da ake zargi ya aikata laifin da misalin karfe 10 na safiyar ranar 6 ga watan Janairu 2021 a mazaunarsa da ke kan titin Ise-Ekiti a Karamar Hukumar Ekere ta Jihar.
- Kotu ta yanke hukuncin kisa kan wanda ya yi wa yaro fyade ya kashe shi
- Shugaban Karamar Hukuma ya nada Hadimai 16 a Jihar Nasarawa
- Gwamnatin Tarayya ta bayar da tabbaci kan ranar komawar makarantu a Najeriya
Insfeta Apata ya ce wanda ake zargi yana shiga hakkin al’ummar da ke zaune a matsugunni daya da shi ta hanyar kunna sauti mai kara wanda ya wuce karfin sauraron kunnuwansu.
Ya ce ganin yadda lamarin ya wuce gona da iri da hana su sakat ya sanya al’ummar yankin suka yanke shawarar cafke wanda ake zargi tare da mika shi zuwa caji ofis a daidai lokacin da ya yi yunkurin satar Akuya a yankin.
Sai dai Insfeta Apata ya kuma bukaci Kotu ta dage sauraron karar domin ya samu damar sake nazartar lamarin da tattaro hujjojin da zai gabatar a zamanta na gaba.
Shi kuwa matashin da ake tuhuma bai amsa laifin da ake zarginsa da shi ba, inda Lauyansa, Mista Ekene Luke, ya bukaci kotu da ta bayar da belinsa tare da ba wa kotun tabbacin ba zai shallake sharudan belin da za ta gindaya masa ba.
Alkaliyar Kotun, Mai Shari’a Taiwo Ajibade, ta bayar da belin wanda ake zargi a kan Naira dubu 50 bisa sharadin gabatar da wanda zai tsaya masa.
Kazalika, an dage zaman kotun zuwa ranar 11, ga watan Fabrairun 2021 domin ci gaba da sauraron karar.