✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da matasa 2 kan yi wa mai cikin wata 8 fyade a Abuja

Matasan sun sace matar tare da yi mata fyade duk da cikin wata takwas da ta ke dauke da shi.

Wata da ke zamanta a yankin Gwagwalada a Abuja, ta tsare wasu makiyaya biyu da suka amsa laifin yin garkuwa da wata mata tare da yi mata fyade a gidan yari har zuwa ranar 22 ga watan Maris.

Mai gabatar da kara, Dabo Yakubu, ya shaida wa kotun cewa a ranar 25 ga watan Fabrairu, wadanda ake zargi, sun yi garkuwa da wata mata mai cikin wata takwas a gidanta da ke Karamar Hukumar Abaji.

Ya bayyana wa alkali cewa wadanda ake zargin sun kuma yi wa matar fyade a cikin dajin, ba tare da la’akari da cewa tan dauke da tsohon ciki ba.

Ya ce wani Abubakar Wakili a Karamar Hukumar Abaji ne, ya kai rahoton lamarin ofishin ’yan sandan yankin Gwagwalada a ranar 26 ga Fabrairu.

Mai gabatar da karar, ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 96, 262, 264, 387 na kundin laifuffuka.

Alkalin kotun, Malam Abdullahi Abdulkarim, ya dage yanke hukuncin ne domin ganin halin da mai juna biyun za ta tsinci kanta a ciki.