An gurfanar da wasu mutane gaban wata Kotun Majistare a Jihar Gombe bisa zarginsu da sacewa da kuma sayar da kananan yara 13 ga masu safarar mutane a Jihar Anambra.
Rundunar ’yan sandan jihar ce a ranar 7 ga Satumba, 2020 ta gurfanar da mutum hudu da ake zargi da haha gungun masu satar yara daga Arewacin Najeriya domin sayar da su a Kudu.
- An kama ‘yan kabilar Ibo 3 kan satar yara a Taraba
- ‘Na gina masallaci da coci da kudin da na samu a satar yara’
An gurfanar da uku daga wadanda ake zargin a kotu yayin da ta hudun ta cika rigarta da iska.
Dan sanda mai shigar da kara, Habibu Juwara ya shaida wa kotun cewa mutanen sun hada baki suka sace kananan yara masu shekaru biyu zuwa biyar —maza 13 da mace daya— a gidaje daban-daban a garin Gombe a shekarun 2018 da 2019.
Ya ce bayan sun sace yaran daga iyayensu sun dauke su zuwa wasu wurare da ba a sani ba inda suka sayar wa masu safarar mutane da su.
Wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin, yayin da dan sandan ya roki kotun da ta dage zamanta domin ya samu damar kammala bincike.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Japhet Maida ya dage sauraron karar har zuwa 29 ga watan Satumba tare da umartar ’yan sanda su ci gaba da tsare wadanda ake zargin.