✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gurfanar da masu gyara a kotu kan zargin satar mota

An gurfanar da wasu masu gyaran mota biyu a kotun kan zargin satar mota kirar ‘Honda Element’ wadda kimarta ya kai Naira miliyan uku. Masu…

An gurfanar da wasu masu gyaran mota biyu a kotun kan zargin satar mota kirar ‘Honda Element’ wadda kimarta ya kai Naira miliyan uku.

Masu gyaran motar, ana tuhumar su da aikata laifuka biyu da suka hada da hadin baki da kuma sata.

Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Edet Okoi, ya shaida wa kotun cewa mutanen sun aikata laifin ne a ranar 24, ga Disamba, 2020.

Okoi ya ce, motar mallakar wata kwastomar mutanen ne bayan ta siyi motar ta kai musu ita gyara.

A cewarsa, mai motar na neman masu gyaran bambar ne bayan ta motarta lalace bayan direban wata motar haya ya daki tata, wanda ya bukaci su je gareji a gyara mata.

Wadanda ake zargin sun caje ta kudin gyara N3,000, kuma ta amince, yayin da ta fita ciro kudin a injin cirar kudi na ATM don ta ba masu gyaran motar, dawowarta ke da wuya sai ta ga samu motar ta yi layar zana.

Da ta tambaye su ina motarta, sai suka ce sun ba wanda ya rako ta garejin mukullan motar.

Jami’in ya ce mai motar ba ta ba su wani bayani da yake nuna cewa ta ce su damka mukallan motar tata ga kowa ba.

Wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifukan da ake cajin su da aikatawa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a, Misis O.O. Oshin, ta bayar da belin kowanne daga cikinsu kan kudi N500,000 su kuma kawo mutum biyu-biyu da za su tsaya musu.

A karshe ta dage zaman sauraren shari’ar zuwa ranar 22, ga watan Fabrairun, 2021.