Wata Babbar Kotun Majistire a Jihar Legas ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai shekaru 45 a duniya da ake zargi da taba nonon wasu ’ya’yansa mata biyu.
Bayanai sun ce mutumin da ake zargi ya fara yi wa kansa tsirara sannan ya rika kai ’ya’yan cafka a mama.
- Majalisa ta mika wa Buhari kasafin kudin 2022
- ’Yan bindiga sun kashe magidanci bayan karbar N1.7m a Zariya
’Yan sanda sun ce lamarin mai cike ta ban takaici ya faru ne a kan titin Sarumi da ke Unguwar Agege a Jihar Legas, wanda nan ne matsugunin mutumin da ’ya’yansa mata biyu.
Aminiya ta ruwaito cewa, mutumin ya fara rufe kansa da ’ya’yansa a cikin daki sannan bayan ya kwale suturar da ke jikinsa, ya rika mulmula nonon ’ya’yan mata biyu da zummar ya motsa musu sha’awa su ba shi damar saduwa da su cikin dadin rai.
Sai dai fa hakarsa ba ta cimma ruwa ba domin kuwa kururuwar da ’yan matan biyu suka rika yi ta ankarar da makwabta har ta kai ga sai da aka balle kofar dakin da karfin tsiya.
“Mutumin da ake zargi ya nemi ya yi lalata da ’ya’yansa ta hanyar taba musu nono bayan ya yi wa kansa tsirara da nufin ya tayar musu da sha’awa, a cewar jami’in dan sanda mai shigar da kara a gaban kotu.
Jami’i mai shigar da kara, Supol Bisi Ogunleye ya ce “bayan an titsiye shi da tambayoyi kuma ya amsa laifinsa, an gurfanar da shi a gaban Kotun Majistire ta Ogba kan zargin aikata laifin cin zarafi.”
Mai sharia E. Kubeienje da ta jagoranci zaman kotun, ta bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyara hali na Kirikiri sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Janairun 2022.