✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gurfanar da likita ya yi wa matar aure fyade a asibitinsa

An gurfanar da wani likita a jihar Adamawa a gaban kotu bisa zargin yi wa wata matar aure fyade.

An gurfanar da wani likita a Jihar Adamawa a gaban kotu bisa zargin yi wa wata matar aure fyade.

Likitan, wanda ma’aikaci ne a Asibitin Kwararru na Jihar da ke Yola, ana zarginsa ne da aikata lalatar a wani asibiti mallakinsa yayin da yake kokarin yi mata gwajin lafiya.

’Yan sanda masu shigar da kara sun gurfanar da shi a gaban Kotun Majistare a birnin Yola ranar Alhamis bisa zargin cin zarafin matar.

A zaman kotun na farko dai, Mai shari’a Aliyu Babawuro ya dage sauraron karar har zuwa 26 ga watan Nuwamba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar ta Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, “Wacce aka yi wa fyaden ce ta shigar da karar wanda hakan ne ya sa jami’anmu suka tashi tsaye domin gudanar da bincike.

“Matar ta shaida mana cewa lamarin ya faru ne lokacin da ta je asibitin ita da mijinta domin neman lafiya.

“Daga nan ne sai muka gayyaci likitan domin ya amsa tambayoyi, daga bisani kuma muka gurfanar da shi gaban kuliya”.