✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gurfanar da hukumar raba-daidai kan son kai a makarantar lauyoyi

Majalisar Wakilai ta gurfanar da Hukumar Raba Daidai ta Tarayya a gabanta bisa zargin nuna fifiko a daukar ma’aikata a Makarantar Bayar da Horon Zama…

Majalisar Wakilai ta gurfanar da Hukumar Raba Daidai ta Tarayya a gabanta bisa zargin nuna fifiko a daukar ma’aikata a Makarantar Bayar da Horon Zama Lauya ta Najeriya.

A ranar Laraba, Babban Sakataren Hukumar, Mohammed Bello ya bayyana a zauren majalisar bayan binciken Ofishin Babban Mai Bincike na Tarayya a shekarar 2015 ya zargi makarantar da dibar ma’aikata a shekarar 2013 ba tare da bin ka’idojin raba-daidai ba.

Da yake jawabi a gaban kwamitin majalisar, babban sakataren ya ce hukumar ce ta amince wa makarantar ta dauki ma’aikata 10 a shekarar 2012. Daga baya kuma ta bukaci karin mutum uku a 2013 wanda ya kai jimlar mutanen 13.

Shugaban kwamitin binciken majalisar Wole Oke ya ce tuni suka kafa kwamitin wucin gadi don binciken zarge-zargen tare da mika rahotonsa cikin makonni biyu don daukar matakan da su ka dace.

Shugaban ya tunatar da Babban Sakataren hukumar cewa aikin hukumar bai tsaya ga sa’ido wajen daukar ma’aikata ba ne kawai, ya kunshi tabbtar da bin ka’idar raba daidai kamar yadda dokokin kasar su ka tanada a ma’aikatu da hukumomin gwamnati.