✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da dan siyasa kan zargin bata sunan Malam Lawan Triumph

Sai dai wanda ake karar Garzali Obasanjo ya musanta laifukan da ake zargin sa da su.

Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Filin Hoki da ke Jihar Kano ta gurfanar da dan siyasar nan Garzali Musa Obasanjo bisa zargin bata sunan Malam Lawan Triumph, daya daga cikin fitattun malaman sunnah a jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa, wani shakikin malamin mai suna Muhammad Sani Abubakar ne ya kai wa ’yan sanda karar Obasanjon kan zargin batanci da taba muhibbar mahaifiyar Malam Lawan Triumph din da ’yan uwansa a shafin sada zumunta na Facebook.

Sai dai wanda ake kara ya musanta laifukan da ake zargin sa da su.

A zaman kotun na ranar Alhamis, bangaren masu kara sun nemi a ba su ranar da za su gabatar da shaidu kan wannan tuhuma ta batanci da ake yi wa Obasanjon.

Kan haka ne Alkalin Kotun, Malam Abdullahi Halliru ya amince da bukatar, ya kuma dage zaman ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Fabrairu 2024.