✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fille kan Shugaban Karamar Hukuma a Imo bayan karbar diyyar N6m

Sun guntule kan ne bayan karbar Naira miliyan shida

Kasa da awa 48 bayan an sace Kantoman Karamar Hukumar Ideato ta Arewa da ke jihar Imo, Chris Ohiu, an tsinci gawarsa ba kai.

Wakilinmu ya rawaito cewa an guntule kan nasa ne ranar Lahadi, bayan wasu ’yan bindiga sun sace shi.

Bayanai sun nuna cewa an sare kan nasa ne bayan an karbi kudin fansar Naira miliyan shida.

An dai sace Chris ne tare da wasu mutum biyu ranar Juma’a a kauyensu da ke Imoko a yankin Arondizuogu. Maharan sun kuma farmaki ilahirin kauyen nasa.

An ce maharan dai sai da suka harbi mutumin a ka kafin su yi awon gaba da shi.

Wakilinmu ya ga wani bidiyon Kantoman yana durkushe da gwiwoyinsa a kasa, yayin da masu garkuwar da shi suke gargadin Gwamnan Jihar, Hope Uzodinma cewa shi ma hakan za ta faru da shi nan ba da jimawa ba.

Bayan sun hallaka Kantoman ranar Lahadi, sun kuma wallafa bidiyonsa ta hanyar amfani da wayarsa a ‘status’ din Whatsapp dinsa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Henry Okoye, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce tuni jami’ansu sun dukufa bincike a kan lamarin.