Gwamnatin Jihar Filato ta girke jami’an tsaro domin dakile yiwuwar ballewar rikici a sassan garin Jos.
An girke ‘yan sandan a sassan garin bayan rikici ya balle a wurin zanga-zangar #EndSARS da safiyar Talata.
Masu rikicin sun farfasa shaguna da gilasan motoci tare da kone-kone a garin na Jos.
Tarzomar ta tashi ne bayan wasu matasa sun tare Titin Ahmadu Bello da ke garin a ci gaba da zanga-zangar #EndSARS ta kin jinin cin zalin da ‘yan sanda ke yi.
Wasu matasa da tare hanyar bai yi musu dadi ba suka kalubalanci hakan, lamarin da ya tayar da husuma a tsakaninsu.