A karon farko, kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Gernot Rohr ya gayyaci dan wasan da ke taka leda a gasar Firimiyar Najeriya, inda ya gayyaci mai tsaron gidan Enyimba, John Noble.
Najeriya za ta buga wasa guda biyu ne, da Benin da Lesotho domin neman gurbin shiga gasar Kofin Nahiyar Afirka na 2021.
- Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba —Monguno
- Kansila ya nada mataimaka 18 a Kano
- An rufe makarantun sakandaren gwamnati a Neja
- Ba zan iya kaskantar da kaina zuwa matakin Wike ba —Raddin Amaechi
Duk da cewa da wuya a samu buga wasan, masu sharhi na ganin gayyatar a matsayin wani cigaba, ganin cewa an dade ana kira ga kocin da ya rika kiran masu kwallo a gida, wanda a cewar wasu zai habaka gasar ta Najeriya.
Sai dai kuma gayyatar Ahmed Musa wanda a yanzu haka yake zaune a gida ba tare da kulob ba a cikin wadanda za su taka leda a wasannin ya bar baya da kura, inda wasu suke cewa bai kamata a kira shi wasan ba.
Sai dai kocin ya ce ya gayyaci Ahmed Musa din ne a matsayinsa na kyaftin, ba wai a matsayinsa na dan wasa ba.
Amma duk da haka, magoya bayan Super Eagles din suna tunani ba a yi adalci ba, musamman duba da cewa Paul Onuachu, wanda yanzu hake yake gaban Messi da Ronaldo a zura kwallaye bai samu shiga ba.
Mene ne ra’ayinku?