Sakamakon yawan ambaliyar ruwa da ake samu a Najeriya da ke haifar da mummunar asarar shinkafa a kasar nan, Cibiyar Bincike da Inganta Iri ta kasa (NCRI) da ke Baddegi a Jihar Neja ta dauki mataki na shawo kan lamarin.
Shugaban Lura da Binciken Irin Shinkafa, Dokta Muhammad Bashir Enagi ya ce, matakin da cibiyar ta dauka shi ne na gabatar da sababbin irin shinkafa masu yawan ’ya’ya wadda kuma ba ta bukatar taki mai yawa kuma take jure fari.
- Kotu ta aike da mawaki Portable gidan gyaran hali
- An tisa keyar mabarata 217 daga Abuja zuwa jihohinsu na asali
A hirarsa da wakilinmu, shugaban ya ce, Cibiyar NCRI ta binciko da kuma gabatar da irin shinkafa daban-daban har guda 68 a Najeriya, inda ta yi musu lakabi da ‘Faro – lines’.
Ya ce, Faro – 66 da kuma 67 su ne irin da suke jure ambaliyar ruwa, domin irin shinkafar zai iya ci gaba da rayuwa ko da ruwan sama ya shanye kansa na tsawon mako biyu, wanda bayan nan za ta iya rubewa, wanda hakan ya bambanta ta da sauran.
Ya kara da cewa, cibiyar ta kuma samar da nau’in irin Faro-68 mai samar da kwaya mai yawa da yalwa idan aka kwatanta shi da tsohon iri da manoma suka saba da shi. “Mun gabatar da iri nau’in Faro-1 zuwa Faro-68. Mun samar da irin shinkafar ne la’akari da yanayin kasar noman daban-daban na Najeriya, inda muke da kasar da take hayi da wadda ke kwari da kurmi.
“Wannan nau’in irin shinkafa idan ruwa ya shafe shi sakamkon ambaliya tsawon mako biyu, da zarar ruwan ya janye shinkafar za ta tsiro ta ci gaba da rayuwa,” in ji Enagi.
Ya ce za a iya samun wadannan irin shinkafa ma jure wa ambaliya a cibiyar da kuma sauran kamfanonin sayar da iri a garin Bidda na Jihar Neja da Kaduna da kuma Kano.