An gano ofishin jakadancin Amurka na bogi a kasar Ghana, wanda aka rufe bayan ya shekara 10 yana bayar da bizar shiga kasar, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana.
“Alamu na nuni da cewa ka shigo ofishin jakadancin Amurka, amma na bogi ne,” kamar yadda Ma’aikatar Harkokin wajen Amurka ta bayyana.
“Ba Gwamnatin Amurka ke gudanar da shi ba, amma an samu tabbacin cewa ’yan Ghana da turkawa ne suka yi hadin gwiwa a wannan aika-aika, tare da wani lauya kwararrre a dokokin kasashe da aikata miyagun laifuka,” a cewar sanarwar da aka baje shafin sadarwar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.
Ginin ofishin jakadancin bogin na dauke da tutar Amurka, tare da hoton Shugaban kasar Amurka Barack Obama a rataye, inda suke bayar da jabun bizar Amurka da mai kyau.
Sai dai bayanai daga sashen harkokin wajen Amurka bai tabbatar da cewa ko wnai ya shiga Amurka da irin wannan bizar ba, ko kuma yaya miyagun suka rika samunta.
Tuni dai jami’an tsaron Amurka da ke ofishin jakadancin Amurka a birnin Accra suka rufe wannan ofishin bogi, kamar yadda sanarwarsu ta tabbatar.