✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gano mai dauke da Coronavirus da ta gudu a jihar Osun

Mahukunta a jihar Osun sun shaida cewa an gano matar nan mai dauke da cutar Coronavirus wacce ta tsere daga inda aka killace ta. Mahukunta…

Mahukunta a jihar Osun sun shaida cewa an gano matar nan mai dauke da cutar Coronavirus wacce ta tsere daga inda aka killace ta.

Mahukunta suka ce matar ita kadai ce ta tsere ba mutum shida ba kamar yadda aka bayyana a baya kuma ana ƙoƙarin gano mutanen da tayi mu’amala da su domin a killace su a yi masu gwajin cutar.

Kwamishinan sadarwa ta jihar uwargida Funke Egbemode, ta shaida haka inda ta bayyana cewa matar na cikin ayarin ‘yan jihar ta Osun da suka dawo daga kasar Ivory Coast a makon jiya, wadanda gwamnatin jihar ta killace ta kuma same wasun su dauke da cutar.

Da safiyar yau Asabar ne aka bayyana tserewar wasu mutum shida daga inda ake kula da su a jihar, lamarin da mahukunta jihar suka ce mace daya ce ta tsere kuma an gano ta ana kuma bibiyar wadanda tayi mu’amala dasu a lokacin da ta tsere.