An gano wurin da haramtacciyar kungiyar IPOB take yada farfaganda ta gidan rediyo tana tunzura mabiyanta domin ballewa daga Najeriya.
Wani rahoto na kafar yada labarai ta CNN ya ce gidan rediyon mai suna Rediyo Biafra yana yada shirye-shiryensa ne ta intanet daga wani gini da ke a yankin Peckham a Kudu maso Gabashin birnin London na kasar Birtaniya.
- Basarake ya rantse da Alkur’ani a masallaci cewa ba ya taimaka wa ’yan bindiga
- Taliban ta haramta aske gemu da jin kida a Afghanistan
“Adireshinsa na nan a yankin Peckham da ke yankin Kudu maso Gabashin birnin London, inda kungiyar take neman raba Najeriya; Kafin a kama shugabanta (Nnamdi Kanu) a Kenya a watan June, magoya bayan Kanu na amfani da tashar Rediyo Biafra da ke Peckham ne wajen yada shirye-shiryensa,” a cewar rahoton na CNN.
CNN ta ce a lokacin da ta ziyarci adireshin, wani mai suna Darlington Imoh, wanda ya gabatar da kansa a matsayin “jami’in kula da watsa shirye-shiryen gangamin kafa kasar Biafra,” shi ne ya tarbe ta a kofar shiga ofishin gidan rediyon a watan Agusta.
Kungiyar IPOB ta kafa gidan rediyon ne domin yada manufarta ta ballewa daga Najeriya da kuma kafa kasar Biafra.
Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, wanda a yanzu yake tsare a hannun gwamantin Najeriya, ya sha amfani da gidan rediyon wajen tunzura mabiyansa kan ballewa daga Najeriya da tayar da yaki.
A ranar 14 ga Yuli 2015, gwamnatin Najeriya ta toshe tashar saboda rashin lasisin yada shirye-shirye.
Daga baya kungiyar, ta hannun gidan rediyon, ta soki matakin da cewa labarin kanzon kurege ne, inda ta fitar da hanyoyin sauraron shirye-shiryenta.
Nnamdi Kanu dai ya yi ta amfani da kafar “wajen yin kira da yaki da kuma yada sakonni masu cike da kalaman nuna tsana ga Najeriya.”