✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gano kifi mai hakora 300

Masana sun ce ba kasafai ake samun irin kofin ba a duniya

An gano wani kifi jinsin Shark da yake rayuwa a kasan teku mai duhu da bai cika bayyana kansa a fili ba mai hakora 300.

Shark, wanda aka fi sani da ‘kasusuwan burbushin halittu’, ya samo asali ne tun miliyoyin shekaru da suka gabata kuma masunta sun yi mamakin ganin nau’in da ba kasafai a baya ake ganinsa ba sai a shekarar 2017.

Kifin ya kasance na tarihi da aka samu da hakora 300 yana ba da haske mai ban-mamaki game da jinsinsa da ba a taba gani ba.

Kifin yana yin iyo a cikin zurfin teku kuma ana kiransa da “kasusuwa mai rai” saboda a cikin shekara miliyan 80 da aka san suna rayuwa a duniya, kifin ya canza.

A cikin 2017, masunta sun yi mamakin ganin irin wannan kifi a lokacin da aka ciro shi daga tekun kusa da Portugal a fiye da kafa 2,000 a kasa.

Yana da hakora 300 da jiki mai tsayi da siririn jiki, shark – din ya bambanta da sauran jinsinsa kamar sauran manyan
fararen kifi – ana bayyana shi a matsayin mai “kamar maciji”, inji mujallar National Geographic, mai nazari kan dabbobi.

Da yake magana da talabijin din SIC Noticisas TV, daya daga cikin masu bincike a lokacin ya ce, suna gudanar da wani shiri a karkashin Kungiyar Tarayyar Turai (EU) don rage yawan kama jinsin kifin don kasuwanci, lokacin da suka ci y karo da daya daga cikin kifin da ba a cika kamawa a duniya ba.

Kifin tsayinsa ya kai kafa biyar kuma an yada hotunansa ta Intanet da suka nuna daruruwan hakora masu ban tsoro da jiki mai tsayi da sirantaka.

Duk da raba hotunan a Intanet da hakoransa masu ban tsoro, irin halittar da ba kasafai ake gani ba, na nuna cewa suna haifar da babbar barazana ga sauran kifaye – suna da mukamuki mai iya kara budewa don kama kifi mai girma.

Mujallar National Geographic ta bayar da rahoton cewa, a cikin wata sanarwa da Cibiyar Kula da Teku da Yanayi ta Portugal ta fitar, a zahiri ba kasafai ake samun irin wannan nau’in kifin ba.

An same shi a cikin ruwan Tekun Atlantika da kuma tekunan Japan da Ostireliya, amma saboda Shark yana
rayuwa a cikin teku mai zurfi kuma ba a cika kama shi ba, masana kimiyya ba su da tabbacin adadinsa a tekun.

Amma an gano wadanda suka samo asali tun miliyoyin shekarun da suka gabata.

Kungiyar Kare Halittu ta Duniya ta lissafa kifin Shark a matsayin nau’in da ba a taba damuwa da shi ba, amma an lura cewa yana girma a teku mai zurfi kuma masu kasuwancin kifi na iya kara yiwuwar kin kama irin kifin da ba a cika so don kasuwancinsa ba.