✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano kasusuwan gawar da suka shafe shekara 31,000 a Indonesia

Ana hasashen dan Adam ya fara tiyata tun a lokacin

Wani sabon bincike ya gano kasusuwan wata gawar matashi da ta shafe kimanin shekara 31,000 a cikin wani kogo da ke kasar Indonesia.

Binciken dai ya nuna sabuwar shaidar da ke alamta wannan ita ce shaidar yanke sassan jikin mutum mafi dadewa da aka taba gani a tarihi.

A baya dai, gawar da aka taba yanke wa hannuwa mafi dadewa a tarihi ita ce wacce aka gano a kasar Faransa mai kimanin shekara 7,000, wacce aka yi amannar tun shekaru aru-aru take.

Binciken dai ya gano cewa a zamanin da gawar ta rayu, lokacin da aka yi amanna shi ne wanda dan-Adam ya fi mayar da hankali a kan noma da farauta, ya nuna tun a sannan mutane na da kwarewa a kan kiwon lafiya da kuma kula da raunuka.

A cewar Tim maloney, wani mai bincike kuma Farfesa a Jami’ar Griffith ta Australiya, “Wannan sabon binciken ya nuna irin ci gaban da aka jima da samu a a bangaren kiwon lafiya a tarihin dan Adam.”

An dai wallafa binciken nasu ne a mujallar Nature a ranar Laraba.

Masu binciken dai na duba yiwuwar kara bincike a kan kogon na Liang Tebo saboda fentin bangonsa mai ban al’ajabi da aka gano a shekarar 20202, wadanda suka kai kusan shekara 40,000.

Kodayake yawancin kasusuwan kwarangwal din suna manne da juna, amma an gano cewa babban dan yatsan kafar hagu da kuma kasan kafar sun cire.

Bayan dogon nazari a kan kwarangwal din, masanan sun gano cewa ba gocewa kasusuwan suka yi ba kuma ba a hatsari suka cire ba, da gangan aka cire su.

Ragowar kashin kafar kuma yana nuna yadda aka yanke shi, kuma babu wata alamar jin rauni da za ta nuna wata dabba ce ta kai wa mutumin hari.

Masana ilimin kimiyya sun ce ba su san me aka yi amfani da shi ba wajen yanke gabar ko kuma yadda aka warkar da shi, amma alamu sun nuna cewa mutumin ya rayu karin wasu shekaru shida zuwa tara a duniya.

Gano kasusuwan dai karin hujjar ne kan cewa dan-Adam ya fara kula da kiwon lafiyarsa tun kafin lokacin da ake hasashe, kamar yadda Alecia Schrenk, wani mai binciken kayan tarihi a Jami’ar Nevada da ke Las Vegas a Amurka ya tabbatar.