✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano karin gawarwakin matafiya 7 a Jos

An gano karin gawarwakin matafiya bakwai wadanda aka kai wa hari sannan aka daddatsa su a hanyar Gada-Biyu da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa…

An gano karin gawarwakin matafiya bakwai wadanda aka kai wa hari sannan aka daddatsa su a hanyar Gada-Biyu da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.

Tun da farko Aminiya ta rawaito cewa akalla matafiya 15 ne aka kashe ta hanyar daddatsa su a cikin wata motar fasinjoji mai cin mutum 18.

Rahotanni sun ce fasinjojin dai na kan hanyarsu ta komawa Jihohin Ondo da Ekiti ne bayan sun halarci wani taron sabuwar shekarar Musulunci da Sheik Dahiru Usman Bauchi ya shirya a Jihar Bauchi.

A wani labarin kuma, Gwamnan Jihar ta Filato, Simon Bako Lalong ya yi Allah-wadai da harin inda ya ce gwamnatin Jihar ba za ta lamunci duk wani yunkurin yi wa zaman lafiyar Jihar zagon kasa ba.

Gwamnan, a cikin martaninsa kan kisan wasu mutanen da basu ji ba, basu gani ba unguwar Rukuba da ke garin Jos, ciki har da wasu matafiya a ranar Asabar, ya kuma umarci jami’an tsaro da su tabbatar sun zakulo wadanda ke da hannu a cikin lamarin domin a hukunta su.

Kazalika, Gwamna Lalong ya kuma yaba wa irin namijin kokarin da jami’an tsaron yankin suka yi wajen yayyafa wa wutar rikicin wuta tare da kama wasu da ake zargi da hannu a ciki.

Gwamnan ya kuma jajanta wa iyalan mamatan tare da bayar da tabbatacin cewa gwamnati zata yi wa tufkar hanci, yana mai shan alwashin ganin wutar rikicin ba ta yadu ba.