✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gano Kananan Hukumomi da ke biyan ma’aikatan bogi albashi a Anambra

 Ezeaka ya ce shugabannin kananan hukumomin da lamarin ya shafa na aikata hakan ne domin kaurara kason da suke samu daga asusun gwamnatin jihar.

Da alama wasu Shugabannin Kananan Hukumomi a Jihar Anambara na biyan albashi ga ma’aikatan bogi a yankunansu.

Shugaban Hukumar Kula da Kananan Hukumomin jihar, Vin Ezeaka, ne ya tabbatar da hakan.

Ya ce wasu Kananan Hukumomin jihar na biyan albashi ga ma’aikata da masu karbar fansho na bogi a yankunansu.

Ezeaka ya ce Ciyamomin Kananan Hukumomin da lamarin ya shafa na aikata hakan ne domin kaurara kason da suke samu daga asusun Gwamnatin Jihar.

Jami’in ya yi wannan tonon sililin ne ranar Litinin a ci gaba da rangadin da yake yi zuwa yankunan Kananan Hukumomin jihar.

Daga nan, ya gargadi ma’aikatan da kananan hukumomin jihar da su guji kowane nau’i na magudi a bakin aiki ko kuma su fuskanci fushin hukuma.