An gano wata jaririyar mai kimanin wata hudu a duniya, da aka sace daga kauyen daga na Karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja, a Jihar Kano.
Mahaifiyar jaririyar, Fatima Kabir, ta shaida wa Aminiya a ranar Juma’ar da ta gabata cewa an sace ’yartata ne mai suna Samhat, lokacin da take wasa da ’yan uwanta a cikin gida, kimanin wata daya da ya wuce.
- An sace uwa da ’ya’yanta hudu a Kaduna —’Yan sanda
- ISWAP ta yi garkuwa da matafiya a hanyar Maiduguri
Fatima dai ta garzaya Kano ne ranar Alhamis, lokacin da aka ankarar da ita wani hoto da ke cigiyar ’yartata a dandalin sada zumunta na Facebook a Jihar Kano.
Wani abokin mijin Fatiman, Ado Musa, lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu ya ce sai dai murnarsu ta koma ciki ne bayan da Dagacin da aka tsinci yarinyar a yankinsa ya ki yarda ya basu ita.
Ya ce har Hakimin Dakwa, Alhaji Alhassan Musa da kansa sai da ya kira daya daga cikin mutanen da ke kula da lamarin a Kano, amma ya ce sun dauki matakin ne bayan wani shi ma ya yi ikirarin cewa jaririyar ’yarsa ce.
Hakimin na Dakwa dai ya ce tuni ’yan sanda suka shiga lamarin, inda dukkan bangarorin suka amince a yi gwajin kwayar halitta na DNA, don gano hakikanin iyayenta.
Da wakilinmu ya tuntubi baturen ’yan sanda (DPO), mai kula da yankin Sabon Wuse, ASP Abdullateef Abiodun, ya tabbatar da sace jaririyar da kuma rahoton tsintarta a Kanon.