✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gano gawargwakin mutanen da ambaliya ta janye a Kwara

Ya zuwa hada wannan labarin, jami'in ya ce ba a kai ga gano inda wadanda lamarin ya shafa suka fito ba.

Jami’an kwana-kwana a Jihar Kwara sun ciro wasu gawarwaki biyu bayan da ambaliya ta ja wata mota zuwa cikin rafi a Akerebiata da ke yankin Ilorin a jihar.

Kakakin hukumar, Mista Hassan Adekunle ya ce an gano gwarwakin mutum biyu da wata mota kirar Toyota Yaris mai lamba: APP544E, a wani rafi da ke daura Kwatar Olusola Saraki a Ilorin.

Ya kara da cewa, “Ji-ta-ji-ta ta nuna lamarin ya faru ne ranar Juma’a da dare lokacin da ake ruwan sama inda matafiyan suka yi kokarin ketare gada wanda a nan ambaliya ta ja su ta yi da su cikin rafi.”

Game da aikin gano gawarwakin, jami’in ya ce aikin hadin gwiwar da aka yi tsakanin jami’ai da mazauna yankin ya taimaka wajen cim-ma nasarar da aka samu.

Daga nan, Adekunle ya shawarci jama’a da su daina tuki yayin da ake ruwan sama mai karfi don kauce wa samun akasi.

Ya zuwa hada wannan labarin, jami’in ya ce ba a kai ga gano inda wadanda lamarin ya shafa suka fito ba.

%d bloggers like this: