✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawar mutum 26 da suka nutse a ruwa a kokarin tsere wa ’yan bindiga

Musayar wuta da aka yi tsakanin ’yan bindiga da jami'an tsaro ce ta razana mutanen kauyen.

Akalla gawarwakin mutanen kauyen Duma da ke Karamar Hukumar Tureta ta Jihar Sakkwato 26 aka tsamo a ruwa.

Rahotanni sun ce, an tsinto gawarwakin mutanen ne wadanda suka nutse a ruwa a kokarin tsere wa ba-ta-kashin da aka yi tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga a wani daji da ke kusa da su.

Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a Larabar da ta gabata, yayin da sojojin rundunar Hadarin Daji suka yi karon batta da wasu ’yan bindigar da suka sato dabbobi a wasu yankuna da ke makwabtaka da Jihar Zamfara.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar DSP Sanusi, hagen ’yan bindiga da kuma harbe-harben musayar wuta ne ya razana mazauna kauyen, lamarin da ya sa suka tarawatse domin neman mafaka.

“Sun [mutanen kauyen] yi zaton ’yan bindigar su suka nufo, wanda wannan lamari ya sa suka razana har wasunsu suka nutse a ruwa.

“Daga baya mun gano gawarwaki mutane 26 kuma tuni an binne su.

Ya ce, “Sun yi zaton ‘yan bindigar da ke gudu ne za su kai musu hari. Sun fara gudu da skelter skelter sakamakon haka wasu daga cikinsu sun nutse. Daga baya an gano gawarwaki 26 da ba su da rai kuma aka binne su.”

DSP Abubakar ya ce har yanzu rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da sintiri a kauyen.

Sai dai ya yi watsi da rahoton cewa ‘yan bindigar sun harbi wasu daga cikin mazauna garin, yana mai cewa, babu wani harbi da aka samu a kan gawarwakin da aka gano.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ce Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya kai ziyarar jajanta wa al’ummar kauyen Duma dangane da aukuwar lamarin.

Gwamnan wanda ya tawagarsa ta kunshi wasu manyan Hafsohin Tsaro na Sojin Kasa, Sojin Sama, ‘Yan sandan da Ma’aikatar DSS ta Jihar, ya jajanta wa al’umma da ‘yan uwan ​​wadanda abin ya shafa.

Ya ce ya je a madadin gwamnatinsa da al’ummar jihar domin jajanta musu kan lamarin.

Tambuwal ya tabbatar wa al’ummar yankin cewa, gwamnati da jami’an tsaro suna bakin kokarinsu wajen ganin an samu zaman lafiya a jihar.

Ya bukaci karin hadin kai daga jami’an tsaro, sannan ya kuma yi addu’ar Allah Ya ci gaba da ba su nasara a kan ‘yan fashi da sauran masu aikata miyagun laifuka.

Gwamnan ya bukace jama’a da su ci gaba tona asirin masu bayar da bayanai ga ‘yan fashi.