Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Rijiyar Zaki a Jihar Kano ta gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan mutumin nan da ake zargi da cinna wa wasu mutane wuta a yayin da suke sallah a garin Larabar Abasawa a yankin Karamar Hukumar Gezawa.
Jerin tuhume-tuhumen sun hada da zargin sanadiyyar kisan mutum 23 da gangan ta hanyar cinna musu wuta a masallaci a garin Gadan wanda aka fi sani da Larabar Abasawa cikin Karamar Hukumar Gezawa.
- An lakaɗa wa Ɗan Bilki Kwamanda duka saboda sukar Gwamnan Kaduna
- Tinubu da NLC sun amince da N70,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci
Sai tuhuma ta biyu da aka karanto masa cewa ya yi yunƙurin kisan wasu mutum biyu a ranar 15 ga watan Mayu 2024 a garin Gadan.
Tuhuma ta uku da ake yi wa Shafi’u kamar yadda kotun ta shaida masa ta ce ya raunata wasu mutane ta hanyar watsa musu fetur a masallaci lamarin da ya yi sanadin haifar musu da munanan raunika.
A tuhuma ta hudu da aka karanta masa, kotun ta ce ya kone masallaci da abubuwan da suke ciki — laifukan da suka saba wa sashe na 143 da 148 da 167 da 370 na Kundin Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta shekarar 2000.
Da alƙalin kotun Ustaz Halhalatul Huza’i Zakaria ya tambayi Shafi’u Abubakar wanda ake tuhuma ko ya fahimci tuhumar sai ya amsa da cewa “E” ya fahimta tare da tabbatar da cewa “lalle haka abin yake ya aikata.”
Bayan haka ne kotun ta ɗage zamanta zuwa ranar 1 da 2 ga watan gobe na Agustar 2024, inda ake fatan za ta yi masa hukuncin kamar yadda masu kara suka nema.
Tun da farko a zaman kotun na yau Alhamis masu gabatar da kara kuma lauyoyin Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Barista Salisu Tahir suka gabatar da sabuwar tuhuma kan Shafi’u Abubakar.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a watan Mayun da ya gabata ne matashin ya banka wa mutane wuta a lokacin da suke sallar Asuba a wani masallaci da ke kauyen Larabar Abasawa na Karamar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano.
Tun dai a zaman da ya gabata ne masu gabatar da kara suka nemi kotun da ta sahale musu su sake gabatar da sabuwar takardar tuhuma ga wanda ake kara duba da cewa adadin mutanen da ake zargin ya cinna wa wutar da suka mutu sun karu bayan da aka fara sauraren shari’ar tasa.
Masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Salisu Tahir sun nemi kotun da ta yanke wa wanda ake kara hukunci kan tuhuma ta biyu da ta uku duba da cewa wanda ake tuhuma ya yi ikirarin aikata laifukan da ake zarginsa da su.
Barista Asiya Muhammad Imam wadda aka turo daga Hukumar da ke bayar da Agajin Shari’a ta Kasa (Legal Aid) a matsayin lauyar wanda ake kara, ta nemi kotun da ta yi wa wanda take karewa sassauci duba da cewa ya amsa laifinsa ba tare da wahalar da kotu ba.
Alkalin Huza’i ya ɗage zaman kotun domin yanke hukunci bisa tuhuma ta biyu da ta uku, haka kuma za a saurari shaidu a game da tuhuma ta daya da ta hudu.
Daga nan kuma ya yi umarni da a ci gaba da tsare wanda ake zargi a gidan gyaran hali.