Gwamnatin Nijar ta sanar da ganin watan Shawwal, wanda ya kawo karshen watan azumin Ramadan a kasar.
Firaiminista Ouhoumoudou Mahamadou ne ya tabbatar da ganin jaririn watan a yammacin Talata kamar yadda sashen Hausa na BBC ya ruwaito.
- ’Yan bindiga sun cinna wa ofishin NDLEA wuta a Abiya
- Ranar Alhamis za a yi sallah — Sarkin Musulmi
- Ahmed Musa zai buga wasan farko a Kano Pillars
Sanarwar ta ce an ga watan ne a cikin yankunan Nijar uku.
Wannan na zuwa bayan Najeriya, makwabciyar Nijar ta sanar da cewa ba a ga watan ba tare da ayyana Alhamis a matsayin ranar Sallah.
Haka kuma, wannan na zuwa ne yayin da wasu kasashen musulmi na duniya suka sanar da rashin ganin watan a yau Talata.
Daga cikin kasashen da akwai Indonesia, Jordan, Malaysia, Qatar, Saudiyya, Turkiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa.