✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ga watan Ramadan a Saudiyya

Za a fara Sallar Taraweeh a Masallatan Harami daga ranar Litinin

Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar da ganin watan Ramadan na shekarar 1442 Bayan Hijira.

Sanarwar ta ce cewar ranar Talata, 13 ga watan Afrilu, 2021, ita ce daidai da ranar 1 ga watan Ramadan a kasar, amma za a fara gudanar Sallar Taraweeh daga ranar Litinin.

“An ga jinjirin wata a kasar Saudiyya, saboda haka 1 ga watan Ramadan, 1442 Hijiriyya, zai kasance gobe Talata ce 13 ga watan Afrilu; Za a fara Sallar Taraweeh, a Masallatan Harami daga bayan Sallar Isha, yau Litinin,” inji sanarwar da hukumomin suka fitar.

An watan ne a kasar Saudiyya yankin Tumai na kasar Saudiyya.

Kazalika wasu kasashen duniya sun ayyana ranar Talata, 13 ga Afrilu 2021 a matsayin ranar 1 ga Ramadan, 1442 Hijiriyya.

Kasashen sun hada da Qatar, Sudan, Jordan, Kuwait, Malaysiya, Indonesiya, Syria da kuma Falasdinu.

A daya hannun kuma, hukumomi sun bayyana cewa ba a ga wata ba a ranar Litinin a kasashen Indiya, Sri Lanka, Australia da kuma Brunei.

A halin yanzu dai a Najeriya ana jiran sanarwa daga Fadar Sarkin Musulumi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, game da ganin watan na Ramadan.