✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ga Daliban Islamiyyar Tegina a Shiroro

An sanar da hukumomi amma har yanzu babu alamar an dauki mataki.

An gano yadda ’yan bindiga ke gararamba a daji da dalibai 136 da suka sace daga makarantar Islamiyyar Salihu Tanko da ke garin Tegina a Jihar Neja.

Majiyoyi sun ce an ga daliban ne a yankin Lakpma na Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar, a yayin da rahotanni suka bayyana cewa uku daga cikinsu sun rasu a hannun masu garkuwar.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Tafidan Allawa, Jibrin Allawa, ya ce, “Ya kamata a gaggauta daukar matakan kubutar da kananan yaran da ke galabaice a cikin Gandun Dajin Allawa.

“An sanar da mu cewa ranar Alhamis da yamma an ga ’yan bindigar da yaran a kan babura a yankin Lakpma a Shiroro sun bi ta Maganda a yankin Pandogari.

“Madaki ya tabbatar mana da ganin yaran a jigace a kan baburan a ranar Lahadi, lokacin da ’yan bindigar suka kai hari kauyen Wutare suka tarwatsa mutanen kauyen da suka shaida mana irin mawuyacin halin da yaran suke ciki.

“Tun daga lokacin muka tuntubi hukumomi amma har yanzu babu alamar an dauki wani kwakkwaran mataki,” inji shi.

Ya yaba wa kungiyar matasa masu kishin yankin Shiroro bisa yadda suke kokarin sanar da gwamnati da hukumomin tsaro halin da tsaro yake ciki a yankin.

Saboda haka basaraken ya kirayi matasan Kananan Hukumomin Rafi da Munya da su yi koyi da takwarorinsu na Shiroro domin samun murya guda domin bayyana halin da suke ciki game da matsalar tsaro da ta ki ci, ta ki cinyewa a yankin.