A ranar Talatar da ta gabata ce Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar da jadawalin sunayen ’yan kwallo guda 23 da za su fafata a gasar Gwarzon dan kwallon duniya da zai gudana a watan Janairun shekara mai zuwa.
Daga cikin ’yan kwallon da aka zakulo sun hada da Gareth Bale da ya fito daga kasar Wales da Karim Benzema na Faransa da Diego Costa na Sifen da Thibaut Courtious dan Beljiyam da Cristiano Ronaldo dan Fotugal da Angel Di Maria na Ajantina da kuma Mario Gotze dan Jamus. Sauran sun hada da Eden Hazard dan Beljiyam da Zlatan Ibrahimobic dan Sweden da Andre Iniesta daga Sifen da Toni Kroos daga Jamus da Philip Lahm daga Jamus da Jabier Mascherano dan Ajantina da Lionel Messi shi ma daga Ajantina da Thomas Muller daga Jamus. Haka kuma akwai Manuel Neuer daga Jamus da Neymar daga Brazil da Paul Pogba dan Faransa da Sergio Ramos daga Sifen da Arjen Robben daga Holand da James Rodriguez dan Kolombiya da Bastian Schweintieger dan Jamus da kuma Yaya Toure daga Kwaddebuwa.
Haka kuma hukumar ta fitar da jadawalin masu horarwa su kimanin 14 da su ma za su fafata a gasar neman Gwarzon kocin shekara. Sun hada da Carlos Ancelotti dan asalin Faransa da yanzu haka yake horar da kulob din Real Madrid na Sifen da Antonio Conte kocin Jubentus da Pep Guardiola kocin Bayern Munich da Juergen Klinsmann kocin Amurka. Sauran sun hada da Joachim Low kocin Jamus da Jose Mourinho kocin kulob din Chelsea na Ingila da Manuel Pellegrini kocin Manchester City da Alejandro Sabella kocin Ajantina da Diego Simeone kocin Atletico Madrid da kuma Louis ban Gaal kocin Mancheter United.