A shekaranjiya Laraba ne Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta Ingila (FA) ta fitar da jadawalin gasar da za a fara a watan Agusta mai zuwa.  Gasar wacce ake wa lakabi da 2014/15 Barclays Premier League ta kasa yadda kungiyoyin kwallon kafa 20 za su fafata tun daga ranar 16 ga watan Agusta mai zuwa.
kungiyar kwallon kafa ta Manchester United wanda sabon kocinta Luis ban Gaal zai jagoranta da zarar an kammala gasar cin kofin duniya za ta fara wasanta na farko ne da kulob din Swansea a gida a ranar 16 ga Agusta sannan ta bi kungiyoyin kwallon kafa na Sunderland da kuma na Burnley kafin ta sake wasa a gida da kueens Park Rangers a ranar 13 ga Satumban bana.  Kulob din ba zai hadu da Chelsea ba sai a karshen watan Oktoba.
Kulob din Mancherter City mai rike da kofin kuwa zai fafata ne da manyan kulob uku ne a farkon makonnin gasar.  Da farko kulob din zai gwada kwanji ne da kulob din Liberpool a gida sai ya bi na Arsenal don karawa da shi sannan ya sake dawowa gida ya hadu da na Chelsea.  Southampton kuma za ta fara wasanta na farko ne da Liberpool a gida. 
An fitar da jadawalin gasar rukunin Premier na IngilaII
A shekaranjiya Laraba ne Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta Ingila (FA) ta fitar da jadawalin gasar da za a fara a watan Agusta mai…