✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fitar da Jadawalin Gasar Cin Kofin kalubale na Ingila

A ranar Litinin da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta Ingila ta fitar da Jadawalin wasan kusa da na karshe (semi-fainal) na gasar…

A ranar Litinin da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta Ingila ta fitar da Jadawalin wasan kusa da na karshe (semi-fainal) na gasar cin kofin kalubale da ake masa lakabi da FA Cup.
Kulob din Chelsea da ya doke na Manchester United da ci 1 mai ban haushi zai kara ne da na Tottenham a yayin da kulob din Arsenal kuma zai kece raini da na Manchester City a wasannin kusa da na karshe (Semi-Fainal).
Wasannin za su gudana ne a ranar 22 ga watan Afrilun 2017 inda daga nan ne za a tantance kungiyoyi biyu da za su kai matakin wasan karshe (Fainal).