✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka farfasa rumbunan abinci a Abuja

Mutum hudu ne aka sanar sun sume a sakamakon turmutsitsin da ya auku

Wasu mutane sun auka wa rumbunan abinci da sauran kayan tallafi a wasu yankunan Abuja bayan zanga-zangar #EndSARS ta sauya riga ta koma barnata dukiyoyi da ma sace-sace.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto a ranar Talata, an fasa dakunan ajiyar abinci da ke unguwar Jabi Daki-biyu, Gwagwa, Gwagwalada da Tungan-Maje a Abuja, sai kuma wanda ke titin Kaduna a garin Suleja, Jihar Neja.

Matasa, yara da ma matan aure sun yi ta yi wa wuraren kawanya suna fasa gine-ginen ko da daye rufin kwanon rumbunan domin kwasar abubuwan da ke ciki.

Masu fasa dakunan ajiyar sun yi awon gaba da kayan abinci, suturu, kayan gini , injunan ban ruwa da takin zamani, wanda ake zaton an tanade su ne domin tallafi.

Dakin ajiyar da aka fasa a na  Jabi Daki-Biyu mallakin Hukumar Agajin ta kasa (NEMA) ne.

Na titin Kaduna kuma ana ganin kayan tallafin COVID-19 ne da wasu kamfanoni su ka bayar, amma aka boye a dakunan ajiya na ‘yan kasuwa.

Aminiya ta nemi jin ta bakin Shugaban Karamar Hukumar Suleja, Abdullahi Shu’aibu Maje a kan lamarin amma ba ta samu nasara ba, amma ya tabbatar da cewa kayan ba na hukuma ba ne.

Wawason da aka yi a Jabi Daki-Biyu da Gwagwa sun wakana ne a ranar Lahadi, na Gwagwalada da Tungan-Maje da Suleja kuma ranar Litinin.

Tun da fari a safiyar Lahadin, matasa sun kutsa rukunin masana’antu da ke Idu, suka fasa manyan dakunan ajiya suka kwashe magunguna da kayan ofis kamar kwamfutoci da kujeru.

Kawo yanzu dai hankula sun koma kan dakunan ajiya da ke Kwali inda rahotanni ake zargin an jibge jami’an tsaro, da na sansanin masu yi wa kasa hidima (NYSC) da ke Kubwa.

Akwai kuma dakunan ajiya da ke Bwari da aka hakikance kayan abinci ne jibge a cikinsu, amma babu matakan tsaro.

Tuni dai Ministan Abuja, Muhammad Musa Bello, bayan wani zaman gaggawa a ranar Litinin, ya ba da umarnin gudanar da bincike a kan lamarin tare da kama duk wanda a ka gani a wuraren ajiyar.

Kafin a fasa wuraren, Minista a Ma’aikatarsa, Ramatu Tijjani Aliyu ta karyata adana kayan tallafin COVID-19 a wuraren, lamarin da ya jawo ayar tambaya a yanzu.

Mutum hudu ne aka sanar sun sume a sakamakon turmutsitsin da ya auku a wurin wawason a Gwagwalada, inda rahotanni suka ce daya daga cikinsu ta rasu.