✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An farke cikin dan acaba a kokarin sace masa babur

Wani barawon babur ya farke cikin wani dan acaba mai shekara 26 mai suna Rabi’u Sani har hanjinsa ya fito a yunkurin da yayi na …

Wani barawon babur ya farke cikin wani dan acaba mai shekara 26 mai suna Rabi’u Sani har hanjinsa ya fito a yunkurin da yayi na  sace masa babur dinsa a garin Bauchi.

Da yake bayyanawa Aminiya yadda abin ya faru aminin wanda aka farke wa cikin, Malam Babangida Chindo, ya ce, mutanen da suka kai masa agaji a lokcin da abin ya faru sun ce suna tafiya ne su biyu a babur kawai sai suka ga babur ya yi cikin daji ya fadi a kasa, sun yi tsammanin hadari ne amma suna zuwa kawai suka tarar suna kokuwa da barawon, kuma ganinsu ke da wuya sai barawon ya gudu lokacin ma har ya farke masa ciki, amma bai yi nasarar daukar babur din ba, daga nan suka dauke shi zuwa wani asibiti da ke Gida Dubu, kafin a zarce da shi zuwa Asibitin Koyarwa Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa.

Ya ce sun kai rahoto ga ’yan sanda kuma rundunar ta tura dan sanda daya asibiti kafin a yi masa aiki.

Ya ce yanzu haka yana ci gaba da jinya a asibitin, kuma an kai babur din gidansu.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, Kamal Datti ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ’yan sanda sun fara bincike a kan lamarin domin kamo wanda ya aikata laifin. Sai ya shawarci ’yan acaba su rika taka-tsatsan da mutanen suke dauka a babur dinsu domin guje wa wanda zai cutar da su.