A ranar Talatar da ta gabata ce Majalisar Wakilai ta Tarayya ta fara yunkurin mayar da farashin fetur zuwa Naira 70, maimakon Naira 145 da ake sayar da shi a halin yanzu.
A kan haka ne majalisar ta bayar da umarni ga Hukumar daidaita farashin man fetur da dangoginsa da ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta mayar da farashin man fetur ya koma Naira 70 maimakon 145 da ake sayarwa a halin yanzu.
dan majalisa Abubakar Hassan Fulata mai wakiltar Birniwa da Guri da kuma Kirikasanma na Jihar Jigawa ne ya gabatar da wannan kuduri.
dan majalisar ya ce a binciken da ya gudanar, ya gano cewa ana kashe Naira 138.11 wajen shigo da man cikin kasar nan ne yayin da aka ba ’yan kasuwa damar sayar da shi a tsakanin Naira 140 zuwa Naira 145. Sai dai ya ce inda gizo ke sakar shi ne, a binciken da ya gudanar ya gano ana kashe Naira 124.54 daga cikin Naira 138.11 kwatankwacin kashi 90 bisa 100 na kudin da ake shigo da man ne ba bisa ka’ida ba.
Ya ce da Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa ’yan kasuwa, musamman a bangaren jigilar man wajen shigo da shi kasar nan, ko shakka babu za a samu raguwar farashi. Hasalima, za a iya sayar da kowace lita a kan Naira 70 maimakon Naira 145.
Ya ce abubuwan da ake ganin suna janyo tashin farashin man fertur suna da nasaba ne da harkokin da suka shafi yin jigilarsa zuwa kasar nan, inda ’yan kasuwar ke samun ribarsu daga masu saye.
Daga nan ne majalisar ta nemi Gwamnatin Tarayya ta rika bayar da agaji ta hanyar saukaka wa ’yan kasuwar wajen shigo da man da hakan zai sa farashin man ya koma Naira 70 a kowace lita.
’Yan majalisar sun amince da kudurin da dan majalisa Abubakar Hassan Fulata ya gabatar kuma nan take suka nemi Ma’aikatar Man Fetur ta kasa (Ministry of Petroleum Resources) ta fara yunkurin rage farashin daga nan zuwa makonni takwas masu zuwa.
Sai dai a nasu bangaren, masu shigo da man sun nuna ba abu ne mai yiwuwa su koma sayar da man a kasa da Naira 145 a wannan lokaci ba, idan aka yi la’akari da yadda Dalar Amurka ke ci musu tuwo a kwarya da kuma yadda darajar Naira ta fadi a kasuwannin duniya. Sun ce wadannan na daga cikin dalilan da suka sa ba za su iya sayar da fetur a kasa da Naira 145 a yanzu ba.
Shi ma a nasa tsokacin, Mai magana da yawun kamfanin matatar mai na kasa (NNPC) Mista Ndu Ughumadu, ya ce ba su samu wani umarni da ya nuna za a rage farashin man daga Naira 145 zuwa Naira 70 daga Majalisar wakilan har lokacin hada wannan rahoto ba.
An fara yunkurin rage farashin fetur zuwa Naira 70
A ranar Talatar da ta gabata ce Majalisar Wakilai ta Tarayya ta fara yunkurin mayar da farashin fetur zuwa Naira 70, maimakon Naira 145 da…