Daga yanzu duk wani mai shiga harabar Majalisar Dokoki ta Kasa sai an yi mi shi binciken kwakwaf a wani mataki na riga kafin tsaro.
Umarnin hakan na kunshe ne a wata wasikar daga Kwamitin Tsaro na Majalisar, wanda Daraktan Gudanrwa Dakta Sani Tahir ya sa hannu.
- Yunkurin dage zabe ya sha kasa * Majalisar kasa ta ki yarda * Hukumar Zabe ta ce ta shirya
- Tsofaffin fuskokin da ba za su dawo Majalisar Tarayya ba
Daraktan ya ce, kwamitin ya yanke shawarar haka ne a matakin riga-kafi, la’akarin da yanayin da ake ciki na tsaro.
“Daga yanzu duk direban motar da zai shigo sai ya fito, ya bude bayan motarsa da kuma cikinta don binciken kwakwaf,” in ji Daraktan Kwamitin Tsaron.
Sai dai wannan bincike bai shafi ’yan majalisar ba, a cewar sanarwar, sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai za su yi amafani da kofar da aka ware ta alfarma in za su shigo majalisar ba.
Matakin ya soma aiki tun ranar Litinin 31 ga watan Oktoba.